Help:Extension:UniversalLanguageSelector/Input methods/ha-tilde
Appearance
A yanzu zaku iya rubutun Hausa da dukkan harrufanta!
Domin yin hakan, sai kubi wannan bayanin:
- Ku shiga akwatin nema da ke a saman shafin.
- Ku latsa alamar keyboard da zai fito a jikin akwatin nema.
- Idan "Hausa" ya fito a saman jerin sunayen, sa ku zaɓi "Hausa - tilde".
- Idan "Hausa" bai fito ba a cikin jerin sunayen, sai kubi bayani mai zuwa:
- Ku latsa alamar "..." dake a ƙasan jerin sunayen. Dan ƙaramin falle zai fito.
- Ku gano "Hausa" a cikin fallen. Ku latsa ta.
- Ku sake latsa alamar keyboard ɗinnan sannan ku zaɓi "Hausa - tilde".
Domin cire wannan keyboard na musamman, ku latsa alamar nan ta keyboard sannan sai ku zaɓi "Use native keyboard" ko kuma ta hanyar shortcut Ctrl+M. Domin sake kuma shiga wurin, sai ku latsa Ctrl+M, ko kuma ku sake bin hanyoyin da aka bayyana a sama.
Domin rubuta haruffan Hausa, ku latsa alamar tilde (~
) daga nan sai ku latsa harafin Latin mafi kusanci da wannan harafin na Hausa. Misali, in kuna son ku rubuta ɓ, sai ku fara sa ~ da kuma b. Ga cikakken jerin su anan ƙasa:
To type this letter... | Type these keyboard keys: |
---|---|
Ɓ | ~B |
ɓ | ~b |
Ɗ | ~D |
ɗ | ~d |
Ƙ | ~K |
ƙ | ~k |
R̃ | ~R |
r̃ | ~r |
Ƴ | ~Y |
ƴ | ~y |
Domin rubuta alamun dake akan haruffa, sai ku fara rubuta harafin, sannan sai tilde (~
) sai kuma ku ƙara da /
, \
, ko kuma ^
.
Domin rubuta wannan harafin... | Ku rubuta wannan haruffan na kan keyboard: |
---|---|
à | a~\ |
é | e~/ |
ô | o~^ |